A Daina Bata Mana Suna Kan Dabinon Saudiyya, Inji Sadiya Farouq

Ku Tura A Social Media
A Daina Bata Mana Suna Kan Dabinon Saudiyya, Inji Sadiya Farouq

Daga Ubaidullah Yahaya Kaura

Babbar kwamishiniyar Hukamar kula da 'yan gudun hijira ta kasa Hajia Sadiya Umar Farouq, ta yi matukar nuna takaicin ta, tare da alhini akan yadda ake ta kokarin batawa Hukamar da take jagoranta, jihar ta haihuwa (Zamfara), ita kanta dama kasar Nijeriya suna akan wai cewa ta karkatar da dabinon tallafi 'yan gudun hjijra da kasar Saudiya ta baiwa Nijeriya sadaka. 

Kwamishiniyar ta bayyyana matukar mamakinta, da takaicinta irin yadda wasu suka yi amfani da kafar sadarwa ta zamani, dama wasu jaridun kasar nan wajen yada labarin kanzon kurege akan cewa ta karkatar da dabinon tallafin zuwa jihar ta haihuwa wato Zamfara.

Kwamishiniyar tace ita dai abunda ta sani shine hukumar ta na iya kokarinta wajen ganin ta kyautatawa 'yan gudun hijira da ma kokarin sauke hakkin da duk ya rataya ga hukumarta. 

Kwamishiniyar ta tabbatar da cewa tabbas 'yan gudun hijira da suka fito daga jihar Zamfara su ma suna daga cikin wadanda suka amfana da tallafin dabinon, domin akwai tarin 'yan gudun hijira da rikicin barayin shanu ya rutsa da su kamar sauran sassa na kasar nan. 

Haka zalika Sadiya ta kara jaddada cewa hukumarta na iya kokarinta wajen daidaito da raba daidai a duk ayukkan da take yi.

Daga karshe kwamishiniyar ta roki al'umma da su kasance masu bincike da tabbatar da labari kafin yada shi.

©Rariya

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"