Rundunar yan sandan jihar Taraba ta kama wani mutum bayan da ya kashe wani dan kaninsa mai kimanin shekaru 4 da haihuwa don maganin kudi

Ku Tura A Social Media
Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta kama wani mutum bayan da ya kashe wani dan kaninsa mai kimanin shekaru 4 da haihuwa don maganin kudi

- Hukumar ta ce zata ci gaba da binciken wannan dan talikin
Malam Abubakar Abdulkadir wanda ya kashe dan kaninsa don maganin kudi

Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta kama wani mutum da ya kashe wani yaro karami ya kuma sara shi gunduwa –gunduwa.

Shi dai mutumin da aka kama mai suna Abubakar Abdulkadir, mai kimanin shekaru 50 da haihuwa da aka fi sani da Sambo, mazaunin kauyen Alin Gora ne dake cikin karamar hukumar Ardo Kola, dubunsa ta cika ne bayan da ya kashe wani dan kaninsa mai kimanin shekaru 4 da haihuwa, ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa kafin daga bisani ya dafa wani sassan jikin yaron.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Mista Yakubu Yunana Babas, wanda shine kwamishinan yan sandan jihar Taraba, ya tabbatar da kama wannan mutum, ya kuma ce zasu ci gaba da binciken wannan dan taliki.To sai dai kuma da yake amsa tambayoyin manema labarai, Abubakar Abdulkadir, ya ce ya dafa naman yaron nema domin yin magani.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta samu nasarar bankado wata maboyar bata gari da suka hada da masu garkuwa da mutane da kuma yan fashi da makamin dake addabar jama’a a jihar, kamar yadda kwamishinan yan sandan jihar ya tabbatar.

Jihar Taraba dai na cikin jihohin dake fama da matsalar masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, batun da kwamishinan yan sandan ke cewa suna samun nasara a yanzu.

Rahoto:naij.com

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"