Osinbajo Ya Rattaba Hannu Kan Muhimman Dokoki Ukku

Ku Tura A Social Media
OSINBAJO YA RATTABA HANNU KAN MUHIMMAN DOKOKI UKU

Mukaddashin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya rattaba hannu kan wasu dokoki uku wadanda fadar shugaban kasar ta ce za su kawo gagarumar sauyi game da yadda ake gudanar da ayyukan gwamnati a Nigeria.

Wata sanarwar da mai magana da yawun Farfesa Osinbajo, Laolu Akande, ya fitar, ta ce daya daga cikin sabbin dokokin, za ta sa ma'aikatun gwamnati su fi bayar da fifiko kan hulda da kamfanoni da kuma 'yan kwangila na cikin gida kan cinikayyar gwamnati.

An kuma sa hannu a dokar da zata saukaka yanayin kasuwanci ga kamfanoni da 'yan kasuwa masu zuba jari ko fitar da amfanin gona daga Najeriya da kuma saukaka shige da fice daga kasar.

Doka ta ukun da Farfesa Osinbajo ya rattaba wa hannu tana neman tilasta wa ma'aikatun gwamnati gaggauta mika bayanan kasafin kudi na shekara uku ga ministan kudi da na kasafin kudi da tsare-tsare a karshen watan Yuli.

Sanarwar ta ce kafin ya rattaba hannu kan dokokin, Farfesa Osinbajo ya gana da ministoci da shugabannin ma'akatun gwamnatin da dokokin suka shafa a fadar gwamnatin kasar.

Sakkwato Birnin Shehu 
19th May, 2017

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"