Motoci Biyu, Gidajen Laka Guda Biyu Da Fam Goma Tafawa Balewa Ya Mutu Ya Bari, Inji Matarsa

Ku Tura A Social Media
Motoci Biyu, Gidajen Laka Guda Biyu Da Fam Goma Tafawa Balewa Ya Mutu Ya Bari, Inji MatarsaMai-dakin marigayi Firayim-Ministan Nijeriya, Sir Abubakar Tafawa Balewa ta ce marigayin ya samu labarin cewa za a kashe shi gabanin juyin mulkin farko da aka yi a kasar.

Sai dai Hajiya Jummai ta shaida wa BBC Hausa cewa marigayin bai dauki wani mataki ba ne saboda ya fawwala komai ga Allah.
Hajiya Jummai ta gaya wa wakilinmu, Is'haq Khalid, irin abubuwan da suke tunawa game da Sir Abubakar Tafawa Balewa:

Ta kara da cewa sun samu labarin rasuwarsa ne daga wajen wazirin Bauchi, Alhaji Yakubu Wanka, mako guda bayan an kashe Sir Balewa a Legas, tana mai cewa a lokacin ita da wasu iyalinsa suna Bauchi.

Hajiya Jummai ta kara da cewa, "Da farko an zo an gaya mana cewa an kashe Sardau, amma shi Firayim Ministan ba a san inda yake ba. Wannan shi ne farkon tashin hankalin da muka shiga. Sai bayan sati daya aka ga gawarsa, mu a lokacin ma ba mu sani ba."

Ta kara da cewa marigayin ya mutu ya bar mota biyu da gida guda biyu na kasa, tana mai cewa kudin da ya bari fam goma ne kawai.

Sai dai ta ce gwamnati ta gyara musu gidan da suke ciki, kuma wasu daga cikin yaransa suna taimaka musu.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"