Mai Babur Dauke Da Man Fetir Ya Jawo Silar Babbakewar Mutane Tara A Yankin Dakatsalle Dake Jihar Kano A Cikin (hotuna)

Ku Tura A Social Media
Mai Babur Dauke Da Man Fetir Ya Jawo Silar Babbakewar Mutane Tara A Yankin Dakatsalle Dake Jihar Kano A Cikin (hotuna)

Wani mai babur dauke da man fetur ya yi sanadiyar konewar wasu mutane tara a yankin Dakatsalle dake karamar hukumar Bebeji a jihar Kano. Inda mutane shida suka kone kurmus, yayin da ragowar guda ukun suke cikin halin rai-kwakwai-mutu'kwakwai a asibiti.

Lamarin wanda ya auku da ranar yau, mai babur din wanda yake dauke da jarkokin man fetur guda biyu, ya bugi wata mota ce a yayin da direbanta ke daukar fasinja a bakin hanya.

Shi dai mai babur din ya yi kokarin kaucewa wata mota ne da ta so ta buge shi, wanda a dalilin haka jarkokin da suke dauke da fetir din suka fashe a kusa da wani mai shayi har ta kai ga fetir din ya kama da wuta, ita ma motar ta kama da wuta dauke da fasinjojin dake cikinta.

Kalli Hotunan Hadarin da abu ya afku Allah ya jikansu da rahama


 Allah Ya jikansu da Rahama ,Allah ya tsare gaba

Rahoto:Rariya

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"