Kungiyar Dattawan Arewa ACF Tayi Allah Wadai Da Hatsaniyar Dake Faruwa Tsakanin Gwamnatin Kano Da Fadar Masarautar Kano

Ku Tura A Social Media
Kungiyar Dattawan Arewa ACF Tayi Allah Wadai Da Hatsaniyar Dake Faruwa Tsakanin Gwamnatin Kano Da Fadar Masarautar Kano

Kungiyar ta bayyana hakanne a cikin takardar bayan taro data fitar jim kadan bayan kammala babban taro na kungiyar, wanda ya gudana a babban ofishin kungiyar dake titin Sokoto a garin Kaduna. 

Dattawan na Arewa karkashin jagorancin shugaban kungiyar tasu Alhaji Ibrahim Commasie Sardaunan Katsina, sun bayyana cewar da akwai wasu makiya ne wadanda suka rura wutar rikici a tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Muhammad Sunusi II kuma abin bakin ciki ne faruwar haka ga dukkanin wani Dan arewa, inda sukayi fatan Allah zai kauda faruwar haka anan gaba. 

Daga karshen taron kungiyar sun kara jaddada mubaya'arsu ga mai girma Shugaba Buhari tare da yin addu'ar Allah ya kara mishi lafiya da tsawon kwana, domin ya dawo ya cigaba da jagorar kasar bisa ga adalci kamar yadda ya saba.

Rahoto Daga :Aminiya

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"