Kotu ta tura Bala Mohammed zaman waƙafi

Ku Tura A Social MediaWata babbar kotun Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ta tura tsohon ministan birnin Bala Mohammed zaman gidan wakafi a gidan yarin Kuje saboda zargin cin hanci da rashawa.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati, EFCC ce ta gurfanar da tsohon ministan a gaban kuliya a kan zarge-zarge shida da suka shafi cin hanci a lokacin da yake kan mulki.

Ana zarginsa da karbar cin hancin N550 million, zargin da ya musanta.

 Mohammed da laifin kin bayyana yawan kadarorin da ya mallaka.
Tsohon ministan ya ce ba shi da laifi.

Alkalin kotun Abubakar Talba ya dage zamanta zuwa ranar 12 ga watan Mayu domin yanke hukunci kan belinsa.

Daga nan ne ya umarci a kai Bala Mohammed zaman gidan wakafi a gidan yarin Kuje.

Rahoto:bbchausa

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"