'Ku daina yadda da jita-jitar mutuwar Shugaba Buhari' -inyi Mai magana da yawunsa mal Garba shehu

Ku Tura A Social Media

Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi Allah-wadai da sabuwar jita-jitar da ake yaɗawa kan mutuwar Shugaba Muhammadu Buhari, tana mai bayyana hakan da cewa wata manaƙisa ce kawai da ake shiryawa don sanya fargaba a zuƙatan 'yan ƙasar.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ne ya yi wannan kira a shafinsa na Twitter.
Ya kuma sake kira ga 'yan Najeriyar cewa, duk wanda ya samu wani bayani a Whatsapp ko Facebook, to kada ya yarda da batun don kuwa 'ƙarya ce tsagwaronta' aka yi wa al'umma don sanya musu fargaba.
Malam Garba Shehu ya rubuta cewa, 

"Ana ta yada jita-jita marar madogara a shafukan sada zumunta cewa wani abu marar daɗi ya faru ga shugaban kasarmu abin kaunarmu Muhammadu Buhari.
"Ba wani abu da ya sami shugaban kasa. Babu wani dalili na damuwa. Mun gode da kiran wayoyin da muka samu."

Shi ma a nasa bangaren, babban mai bai wa shugaba Buharin shawara kan harkar yada labari, Femi Adesina, ya rubuta a shafin nasa na Twitter cewa, "Me ya sa wasu mutanen suke muguwar fata da mugun tunani? Sai abin da Allah ya so ne kawai zai faru. Allah ya albarkaci duk masu yi wa Shugaba Buhari addu'ar alheri."

A watan Janairu ma lokacin da Shugaba Buhari ya tafi birnin London din, an yi ta yaɗa jita-jita a Najeriya cewa ya mutu.

Shugaba Buhari ya tafi Ingila ne a ranar 7 ga watan Mayun nan, don sake ganin likita a kan rashin lafiyar da yake fama da ita, sai dai fadar shugaban ta ce likitoci ne za su fadi ranar da zai kammala ya dawo.
Sai dai kafin tafiyar tasa ya shafe tsawon mako biyu bai fito taro jama'a ba, al'amarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar, inda har wasu kungiyoyi suka dinga kiransa da ya koma ganin likita, yayin da wasu kuwa suke cewa ya yi murabus in ba zai iya ba.

Rahoto:bbchausa

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"