Man Utd za ta girmama 'yan kallon da lantarki ya kashe Nigeria

Ku Tura A Social Media
Man Utd za ta girmama 'yan kallon da lantarki ya kashe Nigeria

Kungiyar kwallo kafar Manchester United ta ce za ta girmama magoya bayanta da suka mutu bayan turken wutar lantarki ya fada kansu a lokacin da suke kallon wasa a birnin Calabar na jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, United ta ce 'yan wasanta za su daura wani bakin kyalle a hannayensu a wasan da za su yi ranar Lahadi "domin tunawa da magoya bayanmu bakwai da suka mutu a kwanakin baya a Calabar da ke Nigeria."
Hukumomi sun ce mutum bakwai ne suka mutu a lokacin da lamarin ya faru, yayin da wasu goma suka samu raunuka.
Sai dai wasu da suka shaida lamarin, sun fada wa BBC cewa adadin ya fi haka, yayin da kafafen yada labarai na cikin gida ke cewa mutum 30 ne suka mutu.

Lamarin ya faru lokacin da jama'a suka taru suna kallon wasan Europa tsakanin Manchester United da Anderletch.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya "kadu kwarai" da jin labarin abin da ya faru wanda ya janyo asarar rayuka.

Rahotanni sun ce gidan kallon ya cika makil da mutane a lokacin da babban layin wutar ya katse, inda ya fado kan jama'a.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"