Barcelona za ta kai karar shugaban Malaga kan kalaman batanci

Ku Tura A Social Media
Barcelona za ta kai karar shugaban Malaga kan kalaman batanci

Barcelona za ta kai karar shugaban kungiyar Malaga Abdullah Al-Thani ga hukumomin wasan Spaniya kan kalaman batanci da tace ya yi mata a Twitter.

Ce-ce-ku-cen ya fara ne lokacin da wani mai goyon bayan Barca ya bukaci Al- Thani a shafin Twitter, kan Malaga ta doke abokan hamayyarsu Real Madrid a wasansu na ranar 21 ga watan Mayu.

Daga nan ne sai shugaban na Malaga ya mayar da amsa inda ya rubuta cikin Larabci ; 

"Da taimakon Allah za mu doke su a fili, amma dattin kumfar Catalonia (ma'ana Barcelona) ba za ta ji kanshin kofin ba, bayan karyar da ta yi a kan koci Michel,".

Shi dai kociyan Malaga Michel ya harzuka magoya bayan Barcelona ne inda ya nuna cewa yana son Real Madrid ta dauki La Liga.

A wata sanarwa da Barcelonan ta fitar ta ce ta nuna rashin yardarta da bacin rai a kan kalaman da shugaban Malaga, Abdullah Al-Thani, ya rubuta a Tweeter, wadanda sun saba wa manufar wasan cikin lumana da kuma dokokin wasanni.
Barca ta kara da cewa: 

"A bisa wannan dalili ne kungiyar za ta gabatar lamarin kwamitin yaki rikici na hukumar wasanni, sanna kuma ta mika batun zuwa ga hukumar kwallon kafa da ta gasar La Liga."

Zakarun na Spaniya, Barcelona da Real Madrid suna kankankan a maki a La Liga, amma Barcan na gaba saboda nasarar da ta fi samu a kan Real din wadda take da kwantan wasa daya.

A ranar karshe ta La Liga, 21 ga watan Mayu, yayin da Real za ta je gidan ta 14 a tebur Malaga, Barcelona za ta kasance a gidanta da Eibar wadda yanzu take ta takwas.
Kocin Malaga Michel ya taimaka wa Real Mad

rid ta dauki kofin La Liga sau shida a shekara 14 da ya yi a Bernabeu.

Daga:bbchausa.com

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"