Mace ,Za Ta Iya Yin Fitsari A Tsaye!!! -Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Ku Tura A Social Media
Mace, Za Ta Iya Yin Fitsari A Tsaye!   !   !  ! 

Tambaya:

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Don Allah malam mene hukuncin yin fitsari a tsaye ga mace ko namiji a Musulunci?

Amsa:

Ya halatta ga namiji ya yi fitsari a tsaye, saboda hadisin da Bukhari  ya rawaito cewa: "Annabi S.a.w ya je jujin wasu mutane sai ya yı fitsari a tsaye"kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi na 222... 
Tare da cewa duk hukuncin da ya zo dağa Annabi s.a w. yana hada mace da namiji, in ba'a samu abin da ya kebance shi ba, Tabbas fitsarin mace a tsaye zai jawo matsala wajan cikar tsarkinta, saboda yanayin halittar da Allah ya yı mata.
 Yana daga cikin Ka'idojin sharia gabatar da wajibi akan abin da aka halatta, yin fitsari a tsaye ya halatta ga mace, saidai zai kai ga kunci wajan tabbatar da Dhahara, wacce sallah ba ta ingantuwa saida ita.

Duk hadisan da suka zo cewa Annabi ya hana yin fitsari a tsaye ba su inganta ba, sai hadisin Nana A'isha wanda HakiM ya inganta, in da take cewa : "Duk wanda ya ce muku Annabi s.a.w ya yi fitsari a tsaye kar ku gaskata shi" kamar yadda  Nasa'i ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 29.
Malamai suna cewa : za'a dau maganarta akan tana bada labari ne, akan abin da ta gani, wannan ba ya kore a samu wani abin daban wanda ba ta sani ba, tun da  ba koyaushe take zama tare da shi ba, yana daga cikin Ka'idoji a wajan malaman Usulul-fiqhi : Duk  wanda ya tabbatar da abu za'a gabatar da maganarsa akan wanda ya kore, saboda wanda ya tabbatar yana da Karin ilimi na musamman wanda ya buya ga wanda ya kore.
Don neman Karin bayani duba : Sharhu Assuyudy ala Sunani Annasa'I 1\26.
Allah ne mafi sani. 

Dr Jamilu Zarewa 


8\3\2016


Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"