Kundin Masu Tuba Fitowa Ta Daya 001

Ku Tura A Social Media
KUNDIN MASU TUBA (001
Akwai wata Mace karuwa (Daga cikin Banu Isra'eel) tana da Sulusin kyawu. wato kamar yadda aka bama Annabi Yusuf (as) rabin kyawu, ita kuma kashi ɗaya cikin uku aka bata. 

Ita Karuwa ce amma Bata yarda wani yayi Zina da ita har sai ya bata Dinare 'dari. 

Akwai wani Mutum mai yawan ibadah watarana ya kalleta ta bashi sha'awa don hala yaje yayi ta aiki da hannunsa yana tara kudin har sai da ya tattaro dinare 'dari din nan sannan ya taho wajenta. 

Ya bata labarin dukkan abinda ya faru, sannan ta umurceshi ya shigo wajenta tana zaune akan wani gadon zinare. 

Har sai da ya kusa afkawa gareta sai ya tuna da tsayuwarsa agaban Allah. Nan take sai tsoro ya kamashi, jikinsa ya rika rawa. 

Sai ya tashi yace mata ki kyaleni in fita na bar miki dinare 'dari din nan. Sai tace "Menene ya faru gareka? Kace na baka sha'awa har kaje kayi aiki da hannunka ka tara wannan kudi, amma yanzu kuma gashi ka samu abinda kake nema amma ka tashi?".

Sai yace "Naji tsoron Allah ne kuma ina tuna ranar da zan tsaya agabansa, Don haka sai naji ina Qinki. Hakika yanzu kece wacce nafi Qi daga cikin Mutane".

Sai Matar tace "In dai abinda ka fada din nan gaskiya ne, to lallai babu wanda yafi chanchanta in aureshi sai kai".

Sai yace "To ki kyaleni dai in fita". 

Tace "Sai dai kayi mun alkawarin cewa zaka aureni".

Sai yace "To ki kyaleni in fita tukunna". Sai tace "To lallai ni nayi alkawarin zan biyoka domin ka aureni".

Sai yace "Watakil"... Sannan ya tashi ya sanya suturarsa ya fita ya koma garinsu. 

Ita kuma wannan Karuwa sai ta fito ta tuba tana yin nadama bisa abinda ta aikata a baya. 

Ta fito har sai da tazo garin da wannan mutumin yake, ta tambayi sunansa da kuma gidansa har aka nuna mata. 

Da aka sanar dashi cewa "Ga wata sarauniya nan tazo nemanka". Yana fitowa da ya kalleta (ya tuno da abinda ya kusa faruwa atsakaninsa da ita) sai yaja numfashi ya fadi akan hannunta ya rasu!. 

Sai tace "To wannan dai ya tsere mun. Amma shin yana da wani Makusanci?". Sai aka ce mata "Ga wani 'San uwansa nan amma Faqiri ne".

Sai tace "Na yarda zan aureshi saboda soyayyar da nake yiwa 'Dan uwansa".

Sai ta aureshi kuma Allah ya albarkaci auren nasu har sai da ta haifi Annabawa guda Bakwai.

Ibnu Qudaamah ne ya kawo wannan Qissar acikin littafinsa "KITABUT TAWWABEEN".

Ya Allah ka karbi tuban al'ummarmu ka gafarta mana zunubanmu ka sanyamu cikin Salihan bayinka ameeen.

Fassara daga Zauren Fiqhu  (14-03-2017).

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"