BREAKING:BABU WANI BATURE DA AKA KAMA A DAJIN SAMBISA - Burutai

Ku Tura A Social Media

BABU WANI  BATURE DA AKA KAMA A DAJIN SAMBISA - Burutai


Shugaban Rundunar Sojan kasa ta Nijeriya, Janar Tukur Burutai ya karyata rahotannin da ake ta yayatawa kan cewa rundunar soja ta kama wani Baturen kasar Faransa a lokacin da rundunar ta fatattake mayakan Boko Haram daga hedkwatarsu da ke Sambisa.

Burutai ya ce, sojoji dai sun kashe wani dan Boko Haram mai jan launin fata amma ba Bature ba ne. Ya kara da cewa hoton Baturen da ake ta yayatawa na wani Baturen Jamus ne wanda sojojin Kamaru suka ceto daga hannun mayakan Boko Haram bayan sun yi garkuwa da shi na tsawon lokaci.

Haka nan kuma, Burutai ya bayyana cewa a lokacin da sojoji suka kaddamar da farmaki kan hedkwatar mayakan Boko Haram, Shugabansu, Abubakar Shekau da shi da manyan makarabbansa sun arce zuwa wata boya wanda kuma a halin yanzu sojojin na ci gaba da farautarsa.

posted:Abubakar Rabi'u
15th January, 2017

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"