MAGANIN CUTAR SIKILA ! ! ! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Tura A Social Media

MAGANIN CUTAR SIKILA ! ! !


Tambaya :
Malam muna da wata yarinya da take fama da cutar sikila, to shi ne mu ka je wajan mai magani , sai ya ce mana mu samu naman kunkuru da jininsa, idan muka yi amfani da shi za ta samu sauki, shi ne muke so mu ji halaccin hakan a wajan malamai ?

Amsa :
To 'yar'uwa Allah madaukakin sarki, bai saukar da cuta ba, saida ya saukar da maganinta, sannan kunkuru yana daga cikin namun da ya halatta a ci, saboda haka idan ya tabbata a likitance cewa namansa yana maganin cutar skila, to za ku iya 

amfani da shi, amma ba za ku iya amfani da jininsa da ya kwarara ba, saboda Allah ya haramta amfani da jinin da ya kwarara,


kamar yadda hakan ya zo a suratu Al'an'am aya ta :145 , amma abin da ya ragu na jini a cikin namansa, wannan ya halatta ayi amfani da shi. 

Masana likitanci suna cewa, sikila wani rauni ne a cikin jini, don haka ba cuta ba ce, balle har ta warke,

amma akwai magungunan da suke rage mata kaifi, daga ciki akwai OSPEN da FOLIC ACID.
Allah ne mafi sani.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"