KA TABA YIN ZINA? |SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

Ku Tura A Social Media

KA TABA YIN ZINA ?

Zina tana cikin manyan laifuffuka, wanda dukkan
shariun da Allah taa'la ya saukar sun hadu akan
haramcin zina,
Al kur'ani mai girma da Sunnar Annabi saw, da
dukkan Malamai sun hadu akan haramcin zina, Kofofin zina guda biyar ne
1- Kallo zuwaga Abinda Allah ya Haramta
2- Shigar batsa
3- Kalaman Batsa
4- kebancewa da matar da ba muharrama ba,
5- Shaawa Mai karfi babu aure Allah taala yace: " kada ku kusanci zina"
Manzon Allah saw yace : Mai zina ba zaiyi zina ba,
yayin da yake zina, sai an cire masa imani.
Abdulllah Dan Mas'ud Ra yace : Duk Al'ummar da
take zina, ta jawo wa kanta fushin Allah, da halaka.
Musulunci yayi umarni da tsare abubuwa biyar, sune : Addini, Dukiya, Rayuka, Hankali, Mutunci,
Nasaba, amma zina ita kadai, tana rusha wadannan
duka,
Hukuncin mazinaci, mai aure kisa ta hanyar jifa,
mara aure Bulala dari da daurin shekara.
Ana tabbatar da zina ta hanya uku, shedu guda hudu, Mutun yayi ikirari da kansa, samun mace da
ciki, babu aure, ko shubha. Bisa sharudda da aka
sanyawa ko wanne.
Zina wata babbar musifa ce da bala'i da dukkan
sharri, da take ruguza al'umma, take wargaza iyali,
take tarwatsa gari, take rushe mutunci, take jawo karayar tattalin arziki, da fatara, da tsiya, da
annoba, a cikin rayuwar dai dai ku, da gidaje, da
unguwanni, da gururuwa, da kasashe, da duniya
baki daya,
Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake samun
dukkan sharri kamar : 1- Raunin Addini
2- Raunin Akida
3-Karancin Imani
4- Rashin kunya
5- Rashin kishi
6- Rashin mutunci 7- Rashin kwarjini
8- Rashin hasken fuska
9- Duhun zuciya
10- Rashin kima
11- Rashin Nagarta
12-Rashin Nutsuwa 13- Rashin Amana
14- Fushin Allah
15- cikawa babu imani
16- Azabar Allah
Allah ya tsare mu da zuriyar mu, da dukkan
al'ummar musulmi daga afkawa zina, wadanda suke yi Allah ya shirye su.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"