INA SHIRIN YIN AURE, SAI TSOHON MIJINA YA CE DAMA CAN YA YI MIN KOME ? | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Tura A Social Media

INA SHIRIN YIN AURE, SAI TSOHON MIJINA YA CE DAMA CAN YA YI MIN KOME ?


Tambaya :
Malam mijina ya sake ni bayan na kammala idda, saura kwana uku na yi aure sai ya zo ya ce dama ya yi min kome, amma bai sanar da ni ba ne, don Allah malam yana da hakki, ko kuma na kyale shi na yi aurena ? saboda gaskiya ina son wancan, amma kuma ba na so na sabawa sharia ?

Amsa :
To 'yar'uwa tabbas miji yana da damar da zai yiwa matarsa kome mutukar tana cikin idda, kamar yadda aya ta :228, a suratul bakara take nuni zuwa hakan, Amma mutukar bai yi mata kome ba har ta kammala idda to ba shi da dama akan ta, amma zai iya shiga cikin manema.

Idan ya yi da'awar cewa ya yi mata kome tun tana idda, amma bai sanar mata ba ne sai bayan ta kammala idda, to ba za'a gaskata shi ba, sai ya kawo shaidu, wadanda za su tabbatar da faruwar hakan.

Yana daga cikin ka'idojin sharia toshe duk hanyar da za ta kai zuwa barna, idan aka bar abin a bude, wanda yake kin matarsa, zai iya mata mugunta, ta wannan hanyar, hakan yasa malamai suka ce sai ya kawo shaidu za'a gaskata shi, idan kuma bai kawo ba za ta iya zuwa ta yi auranta .

Saidai wasu malaman suna cewa : idan har matar ta gaskata shi, to ya isa, ko da bai kawo shaidu ba .

Duba : Al-mabsud 2\23 da Mawahibul-jalil 5\408

Allah ne mafi sani.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"