HUKUNCIN AUREN YAHUDU KO NASARA | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Tura A Social Media

HUKUNCIN AUREN YAHUDU KO NASARA


Tambaya :
Malam musulmi zai iya auren ahlul-kitab tana addininta yana musuluncinsa ?


Amsa :
To dan'uwa Allah madaukaki ya halatta auren ahlul-kitabi, wato Yahudu ko Nasara, kamar yadda ya yi bayanin hakan a cikin suratul Ma'ida aya mai lamba ta :
(5),


kuma an samu wasu daga cikin sahabai, sun aure su kamar Usman dan Affan - halifa na uku a musulunci- ya auri Banasariya, haka Dalhatu dan Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa ya auri Bayahudiya, Allah ya kara musu yarda. duba : Ahkamu-ahlizzimah 2\794


Saidai malaman wannan zamanin suna cewa, abin da ya fi shi ne rashin auren Ahlul-kitab saboda yadda zamani ya canza, domin da yawa idan mijinsu musulmi ya mutu yaran suna zama kirista, kai wani wani lokacin ko da sakinta ya yi zata iya guduwa da yaran, sannan zai yi wuya ka samu kamammu wadanda ba su taba zina ba a cikinsu .Wasu kasashen kuma idan za ka auri kirista daga cikinsu dole zai ka yarda da dokokin kasarsu, a lokuta da yawa kuma za ka samu dokokin sun sabawa ka'idojin musulunci .

Allah ne mafi sani.

  Amsawa

Dr jamilu zarewa

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"