BA KOWACCE RANTSUWA AKE YIWA KAFFARA BA!! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Tura A Social Media

BA KOWACCE RANTSUWA AKE YIWA KAFFARA BA!!

TAMBAYA:
Assalamu alaikum warahamatullah, dan Allah inaso a amsa min wannan tambayar:-shin kowata irin rantsuwa ce ake yin mata  kaffara kokuwa ba kowace bace ake yiwa kaffara ba ? na gode.
AMSA:
Wa alaikum assalam, ba kowacce rantsuwa ake yiwa kaffara ba,  rantsuwoyi a fiqhun musulunci iri uku ne:
1. Rantsuwar da aka yi akan karya, wannan tana iya turbutsa mutum zuwa wuta, ba ta da kaffara sai istigfari, saboda girman zunubinta.                                                                                                                                            
2. Rantsuwar da ta zo baki yayin magana ba tare da nufi ba, wannan Allah ya yi afuwa akanta, kamar yadda ya bayyana a aya ta: 224 a Suratul Bakara.          i                                                                              
3.Rantsuwa akan wani abu da zai zo nan gaba, kamar ya ce : wallahi gobe zan je wuri kaza, in bai je ba, zai yi mata kaffara, kamar yadda aya ta: 89 a suratul Ma'ida ta tabbatar da hakan.                                                                                                                 
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"