ZAN IYA AURAN WANDA IYAYANSA BA MUSULMI BA ?|DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Tura A Social Media
*ZAN IYA AURAN WANDA IYAYANSA BA MUSULMI BA ?*
*_Tambaya:_*
Assalamu alaikum, Dr ya halatta mace ta auri wani wanda Baban shi ba musulmi ba ne?, amma Mahaifiyar shi musulma ce?
*_Amsa:_*
Wa alaikumus salam,  Ya hallata mana ko da kuwa duka iyayansa arna ne.     
Babban abin lura a wajan aure shi ne addinin Wanda ya zo neman aure, saboda fadin Annabi, sallallahu alaihi wa sallama: *_"Idan Wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa"._* Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1084, kuma Albani ya kyautata.
In kika lura za ki ga hadisin ya yi magana ne akan mutumin ba iyayansa ba.                                                                Akwai sahabban Annabi, sallallahu alaihi wa sallama, da yawa wadanda iyayensu ba musulmai ba ne, amma wannan bai hana a aura musu 'ya'ya ba, irinsu Sayyadina Aliyu bn Abu-Dalib da Abu-Ubaidah da saurasu.           
Mahaifin sayyidina Aliyu Abu-dalib bai musulunta ba, Amma kuma an aura masa shugaban Matan Aljanna Nana Fadima, Allah ya kara yarda ga mata da mijin.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa: *_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*
12/11/2016

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"