Kuma dai? Yanzu-Yanzu: Bama-bamai sun tashi a Maiduguri

Ku Tura A Social Media
Rahotanni daga birnin Maiduguri da ke jihar Borno ta Najeriya na cewa wasu bama bamai sun tashi da safiyar ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba
.
Harin kunar bakin wake a Maiduguri
Ganau sun shaida wa majiyar mu ta BBC cewa lamarin ya faru ne a tashar motar Muna da ke cikin birnin.
Wani da ya shaida lamarin ya ce wanda bama-baman sun tashi ne a daidai lokacin da muke shirin shiga motoci domin tafiya zuwa garin Gamborou.
Har yanzu dai babu cikakken bayani kan asarar rayuka da jikkata sakamakon tashin bama-baman. Babu wanda ya dauki alhakin harin kawo yanzu, amma birnin na Maiduguri dai ya sha fama da hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram.
Sai dai an dade ba a samu rahotannin tashin bama-bamai a birnin ba.
Sojojin kasar dai na cewa sun ci lagon ‘yan kungiyar ta Boko Haram sakamakon fatattakarsu da suke yi. Amma shugaban wani bangare na kungiyar, Abubakar Shekau, wanda ya fito a wani sabon bidiyo kwanakin baya, ya ce har yanzu suna nan da karfinsu.
Kawo yanzu jami’an tsaro ba su ce komai game da lamarin ba.
A kwanan baya ne dai Rundunar Sojin Najeriya ta mayar da martani kan wani faifan bidiyon da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar, a inda ya karyata sojojin kan cewa sun raunata shi.
Da sanyin safiyar ranar Lahadi ne dai kungiyar ta saki faifan bidiyon a shafin intanet.
A cikin bidiyon, Abubakar Shekau ya kwashe kimanin minti 40 yana magana da harsunan Hausa da Larabaci da Turanci da kuma Kanuri. Da fari dai ya karyata rundunar sojin Najeriya da ta bayar da sanarwar raunata shi a wani harin sama da ta ce ta kai kan ‘yan Boko Haram.
Shekau ya ce yana nan lafiya kalau babu abin da ya same shi. Hakan ne ya sa rundunar sojin ta Najeriya, ta mayar da martani, a inda ta bayyana kalaman Shekau da rashin hankali.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"