Kudurin Daidaito Ga Maza Da Mata A Najeriya Ya Sami Karatu Na Biyu A Majalisar Dokoki

Ku Tura A Social Media
Wasu ‘yan Majalisar Najeriya na kiran nuna fahimta ga Majalisar Dattawan musamman kan kudurin dokar daidaito ga maza da mata a wajen ilimi, gado, aure, mukamai da dai sauransu, wanda ya kai karatu na biyu a majalisar.
Kudurin wanda Sanata Abiodun Olujimi ta gabatar, ya sami suka mai tsanani daga malaman Islama da nuna sashin kudurin ya sabawa tanadin addinin musulunci. Sanata Olujimi, wacce ta taba gabatar da kurudin a watan Yuni amma bai sami nasara ba, ta sake kawo batun da nuna ana cin zarafin mata a Najeriya duk da kasar ta rattaba hannu kan kudurori daban daban na ‘yancin mata a MDD.
Yanzu haka dai kudurin ya samu goyon bayan Majisar Dattawan zuwa karatu na biyu, amma Sanata Mohammad Ubali Shitu daga jihar Jigawa yace sam bai amince da sashen kudirin ba. wanda kuma yace kudurori marasa amfani irin wannan zasu tabbatar da cewa basu shiga dokar Najeriya ba.
Malaman Islama dake kira ga al’umma kar su dauki wani matakin hatsaniya don baiwa ‘yan Majalisar uzuri da lokaci, sun bukaci kawar da sashen kudurin. Imam Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar Ahlus Sunnah a Najeriya, yace “duk wanda ya samu kansa a Majalisa kar ya manta kuma bayan yana ‘dan Majalisa dole yana da addini ko ya zamanto musulmi ko krista.”
Shin wannan kuduri zai wuce karatu na biyu? Yanar gizo dai ta cika da martani daga manyan malaman Islaman Najeriya kan kin jinin kudurin. Kafofi sun ruwaito Sheik Dahiru Bauchi da Sheik Karibullah Nasiru Kabara na togaciya ga ‘yan Majalisa kan su jingine kudurin.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"