Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Shigo da Shinkafa ta Iyakokinta

Ku Tura A Social Media
Gwamnatin Najeriya ta fito ta bayyana manyan dalilan da suka sa har yanzu tana cigaba da hana shigowa da shinkafa kasar ta iyakokinta.
Baicin dalilin habaka shuka shinkafa a cikin gida akwai kuma dalilin hana shigowa da gurbatacciyar shinkafa wanda ya saba faruwa can baya.
Babban kwantrolan hukumar hana fasakwauri Kanar Hamid Ali yace gwamnati na barin a shigo da shinkafar ta teku inda hukumar kula da lafiyar abinci da magunguna NAFDAC take da kayan gwajin shinkafar da ta shigo ta teku.
Yace batun shinkafa an dade ana kai da kawowa.Wadanda yakamata su sani sun sani wadanda kuma saboda rashin sani suna ta yin korafe korafen da basu kamata ba. Yace ainihin gaskiyar ita ce gwamnati bata hana shigowa da shinkafa ba. Sai dai ta hana shigowa da shinkafa ne ta iyakokin kasa.
Kanar Hamid Ali yace akwai gurbatacciyar shinkafa dake shigowa ta iyakokin kasar saboda NAFDAC bata da naurorin gwaji akan iyakoki. Naurorin gwajinta suna tashoshin teku ne. Dalili ke nan da gwamnati ta ce duk wanda zai shigo da shinkafa sai dai yayi anfani da hanyar teku inda NAFDAC zata iya yin gwajin da ya dace su tabbatar shinkafar lafiyayyiya ce kuma ana iya cinta.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"