DUKIYAR KASA TA GWAMNATI CE!!!|DR.JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Tura A Social Media
DUKIYAR KASA TA GWAMNATI CE ! ! !
Tambaya?
Assalamu alaykum, malam da fatan kana lafiya,
Tambayata itace :-
Shin wa yake da ikon tasarifi cikin dukiyar kasa, gwabnati kadai ko talakawa ma suna da rabo a ciki ?.
Saboda Na ji wani Malami a Radio yana cewa dukiyar kasa ta gwabnati ce, talaka baya da rabo a cikin ta.
Kubamu fatawa Allah shi saka muku da Alkairi.
Amsa :
Wa alaikum assalam, Shugaba shi ne yake da ikon tasarrufi a dukiyar kasa, saidai ya wajaba amfanin da zai yi da dukiyar ya zama gwargwadon maslahar talakawan da yake mulka saboda fadin Annabi S.a.w. (Dukkanku masu kiwo ne, kuma za'a tambaye ku akan abin da kuke kiwo) kamar yadda Muslim ya rawaito.                                                        Tabbas Allah zai tambayi Shugaba idan ya barnatar da dukiyar al'uma ba bisa ka'ida ba.
Bukhari ya rawaito hadisi, Annabi S.A.W. yana cewa: (Tabbas za ku yi kwadayin shugabanci amma kuma zai zama nadama, madalla da darbar da za'a samu a lokacin shugabanci, saidai abin da zai biyo baya a lahira ya munana),  wannan yana wajabtawa Shugaba taka-tsantsan da kuma tuna lahira idan yana kan kujerarsa.                           
Allah ne mafi sani:
27/10/2016
DR. JAMILU ZAREWA

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"