To fa! MTN a ciki matsala, za ta sha bincike (Karanta dalili)

Ku Tura A Social Media
A ranar Talata, 27 ga watan Satumba ne ‘yan majalisar dattawa a Najeriya suka amince a gudanar da bincike a kan zargin cewa kamfanin sadarwa na MTN ya fitar da kudin da yawansu ya kai dala biliyan 13.92 daga kasar ta haramtaciyyar hanya.

Sai dai zuwa yanzu kamfanin na MTN ya ki cewa komai a kan wannan shawara da majalisar ta yanke.
Mutane miliyan 62 ne dai ke amfani da layukan MTN a Najeriya, lamarin da ya sa kasar ta zama kasuwarsa mafi girma a Afirka.
Zuwa bayan sallar azahar a ranar Talatar dai darajar hannayen jarin kamfanin ta yi kasa da sama da kashi hudu cikin dari.
Ba dai wannan ne karon farko da kamfanin MTN ke takun-saka da hukumomin Najeriya ba.
A watan Oktoban bara ma, hukumar da ke sanya ido a kan kamfanonin sadarwa, NCC, ta ci tarar kamfanin dala biliyan biyar saboda ya ki rufe layukan mutanen da ba su yi rijista ba har wa’adin da aka diba domin yin rijistar ya wuce.
Sai dai daga baya hukumar NCC din ta rage tarar zuwa dala biliyan uku da miliyan dari hudu.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"