SHIN YA HALLATA NA YIWA WANI DAWAFI ?|Dr jamilu zarewa

Ku Tura A Social Media
SHIN YA HALLATA NA YIWA WANI DAWAFI ?
Tambaya :
salam malam yayata ta jidda ta ce in tambaye ka menene hukuncin yin dawafi ga wani, saboda mutane suna yawan bugowa suna cewa a musu dawafi, kuma ta ce in gaya ma wai don Allah ka amsa a face book, saboda ana bukatar sanin amsar.
Amsa :
To 'yar'uwa babu wani dalili ingantacce wanda yake inganta yiwa wani dawafi, sannan kuma ba'a samu magabata na kwarai suna yi ba, ga shi kuma dawafi ibada ce, ita kuma ibada ba'a yin ta sai da dalili daga Alqur'ani ko Sunna, amma dai ana iya yiwa wani addu'a lokacin da mutum yake yiwa kansa dawafi.
Akwai dalilai da yawa wadanda suke nuna ingancin yiwa wani Umara ko Hajji, saidai ba'a samu na dawafi a karan kansa ba.
Kiyasin dawafi akan Hajji da Umara ba zai yiwu ba, saboda dawafi tsantsar ibadar jiki ce, hajji da umara kuma ibadu ne da suka hada jiki da dukiya, duk ibadar da ta hada jiki da dukiya, tana amsar wakilci, amma wacce ake yin ta da jiki kawai ba ta amsar wakilci kamar sallah.
ALLAH NE MAFI SANI
Duba Fatawaa Nurun Aladdarb mai lamba ta : 87
Jamilu Zarewa
7\12\2014

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"