'Yan sanda sun tarwatsa zanga-zangar 'yan Shi'a a Abuja

Ku Tura A Social Media
Kungiyar 'yan Uwa Musulmi wacce aka fi sani da 'yan Shi'a a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja, babban birnin kasar domin kira ga hukumomi su saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

'Yan kungiyar sun koka kan yadda jami'an tsaron kasar ke ci gaba da tsare shugaban nasu tun watan Disambar 2015.
A cewarsu, bai kamata a ci gaba da tsare shi da wasu manyan mabiyansa ba, musamman ganin cewa ba shi da lafiya sakamakon raunin da suke zargin sojoji sun yi masa a lokacin da suka kai farmaki a gidansa da ke Zaria a jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna 'ya'yan kungiyar na gujewa hayaki mai sa hawaye da 'yan sanda suka watsa musu.
A watan na Disamba ne dai aka yi arangama tsakanin 'yan kungiyar da sojojin Najeriya bayan sojin sun yi zargin cewa 'yan Shi'a sun yi yunkurin halaka shugaban sojin kasa, Laftanar Janar Yusuf Buratai.
Sai dai 'yan kungiyar sun musanta zargin, suna masu cewa sojoji sun kashe dubban mabiyansu

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"