MANOMI ZAI IYA SAYAR DA HATSINSA KAFIN YA GIRBE ?

Ku Tura A Social Media
MANOMI ZAI IYA SAYAR DA HATSINSA KAFIN YA GIRBE ? Tambaya: Assalamu Alaikum. Mutum ne yake bada kudin Gero ga manoma tun kafin ma amfanin ya girma. Misali, in ana saida Gero a lokacin shifka #450, to sai suyi lissafi akan tsammanin Geron zai sauko zuwa #150. Kaga duk #450 daya ba manomi, zai kawo mai Tiya 3 ta Gero kenan. Menene halaccin wannan ciniki ? Amsa: Wa alaikum assalam, Ya halatta mutukar sun cimma daidaito akan hakan, wannan shi ake kira Salam a wajan malaman Fiqhu(Kan ta gasu), Annabi (s.a.w) da ya zo Madina ya samu mutanen garin suna wannan cunikayyar, sai ya ce musu: (Duk Wanda zai yi, to ya yi a cikin Ma'auni sananne, zuwa lokaci sananne) . Allah ya halatta wannan nau'i na cinikayya saboda saukakawa mutane, Manomi zai iya bukatar kudi kafin amfaninsa ya zo. Allah ne mafi sani. Amsawa: Dr jamilu zarewa.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"