Dubi manyan kamfanoni na duniya dake neman Buhari a birnin New York

Ku Tura A Social Media

– Ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa kasar Amurka ya ja hankalin masu hannun jari da dama da ke so ganawa ta sirri da shi
– Ywancin Kamfanonin suna shirin zuba hannun jari a kasar Najeriya suna kuma neman goyon bayan gwamnati
– Shugaban kasar yayi alkawari cewa kasar Najeriya tana da sama da dama da zata amfana daga ciki
Duk da koma bayan tattalin arziki da kasar Najeriya ke fuskanta, da alama akwai haske a cikin rayuwarta nag aba kamar yadda manyan hukumomin duniya suke ta neman ganawa na sirri tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a birnin New York na kasar Amurka.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na magana a taron bangaren kasuwancin Amurka da Afrika
Shugaban wadda ya halarci taron majalisar dinkin duniya yayi amfani da damar ya fada ma duniya gaba daya cewa kasar Najeriya na da babban iko ta kuma bude fili ga masu zuba hannun jarí
Buhari ya kuma yi Magana a taron bangaren kasuwancin Amurka da Afrika, inda ya tallata kasar Najeriya ga masu zuba hannun jari.
A cewar Sahara Reporters, da alama tafiyar kasar Amurka wanka ya fara biyan kudin sabulu kamar yadda shugabannin kamfanoni suka fara neman ganawa tare da Shugaban kasa Buhari.
Wasu daga cikin kamfanonin sun hada da Motorola, MasterCard, Visa, Proctor da Gamble, da kuma kamfanin Africa Finance Corporation (AFC).

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"