Attahiru Bafarawa ya rubuta wasika ga Shugaba Buhari

Ku Tura A Social Media
– Tsohon gwamnan jihar Sokoto a karkashin Jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP), Attahiru Bafarawa
– Bafarawa tsohon gwamna ne a Jam’iyyar ANPP, wanda daga baya zama cikin Shugabannin ta, itace kuma Jam’iyyar da ta far aba Shugaba Buhari tikitin tsayawa takara a kasar nan

Shi kan sa Attahiru Bafarawa, ya taba neman takarar Shugabancin Kasar a karkashin Jam’iyyar DPP. Bafarawa ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da yadda zai samu nasara a mulkin sa. Idan ba a manta ba, Attahiru Bafarawa yana cikin iyayen gidan Jam’iyyar APC lokacin da aka kaddamar da ita, sai dai, daga baya ya fice abin sa.
Alhaji Dalhatu Attahiru Bafarawa yace wannan ne karo na hudu da ya rubuta wasika zuwa ga Shugaban Kasar Najeriyar, Muhammadu Buhari. Sai dai wannan karo Attahiru Bafarawa yace ya rubuta wasikar ta sa a bude. A cewar tsohon Gwamnan dai Kasar na fama da tarin matsaloli, don haka dole a sa hannu gaba daya wajen ceto Kasar.
Attahiru Bafarawa yaba Shugaba Buhari shawarar cewa ya duba wajen Jam’iyyar sa ta APC domin neman wadanda za su iya kawo karhsen matsalar da Kasar ta ke ciki. A cewar sa bah aka Shugaba Jonathan yayi ba, kuma bai zargi shugabannin baya ba. Bafarawa yace dole Buhari ya rika matso da Gwamnonin adawa jika, duba da irin yadda Shugaba Obasanjo yayi da Gwamna Bakura na Zamfara a lokacin sa. Yace dole kuma Buhari ya rika karbar shawara dage mutane da dama, musamman wadanda suka taimaka masa ya samu wannan matsayi.
Attahiru Bafarawa ya kuma kira Shugaba Buhari da ya karfafa Hukumar EFCC domin yaki da rashawar ya fi da. Kuma idan abin da gaske ne, a binciki ‘Yan Jam’iyyar sa ta APC, musamman wadanda suka tsero cikin ta don samun mafaka.
Tsohon Gwamnan Jihar Sokoton, Attahiru Bafarawa yace dole Buhari ya shirya jin suke daga bakin Jama’a duk kuwa dacin hakan.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"