ZAN IYA YIWA MAMACI AIKIN HAJJI ?

Ku Tura A Social Media
ZAN IYA YIWA MAMACI AIKIN HAJJI ?
Tambaya:
Assalamu alaikum wa rahmatullah, Malam Barka da dare, Malam ina tambaya ne dangane da wakilci a aikin hajji (Anniyaabatu anil mayyit), mahaifina yana son yiwa wani daga cikin makusantan shi da ya rasu; sai wani mutum (malami) yake ce masa ai akwai addu'ar da ake yi (qul huwal laahu sau wani adadi dss) wadda tafi wannan aikin hajjin da za ai masa!!
To dan Allah Malam yana so ne yaji shin hakan ya tabbata, kuma dai-dai ne? , ko akwai wani Malami da ya fadi hakan?
Amsa:
Wa alaikum assalam,Ba haka ba ne, wannan maganar ba ta da asali, Yiwa wani hajji ya tabbata a hadisai, wani mutum ya tambayi Annabi (s.a.w) cewa: "Babana ya mutu bai yi hajj ba, zan iya yi masa?, sai Annabi (s.a.w) ya ce yaya kake gani Idan da bashi ya bari za ka biya masa?,sai yace E,sai Annabi (s.a.w) yace to ai bashin Allah shi ya fi cancanta a biya, don haka ka yi masa hajji, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya rawaito a Muntaka a hadisi mai lamba ta: 1797, da kuma Darakudni.
Sannan Kathamiyya ta tambayi a Annabi (s.a.w) cewa : Hajji ya riski babanta yana tsoho za ta iya yi masa? sai Ya ce E, kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta ; 1756.
Malaman fiqhu sun kafa hujja da Wadannan hadisan tabbatattu akan halacci ko wajabcin yiwa mamaci ko Wanda ba zai iya ba aikin hajji Idan yana da halı.
Hajji ibada ce mai zaman kanta,kuma daya daga cikin ginshikan musulunci babu yadda za'a yi wata addu'a ta zauna a makwafinta.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.
29\4\2016

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"