FATAWAR RABON GADO (47) DR.JAMILU ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (47)
Tambaya:
Assalamu Alaikum dr. Mutum ne ya rasu bai yi aure ba, ya bar mahaifiyarsa da yayarsa uwa daya uba daya da kuma kanwa mace daya wacce suka hada uba daya, to ya rabon gadonsa zai kasance? .nagode
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida:5, a bawa babarsa kashi:1, sai 'yar'uwarsa shakikiya ta dau kashi:3, wacce suka hada uba daya kawai ta dau kashi dayan da ya rage.
Allah ne mafi Sani:
Dr Jamilu Zarewa
16/08/2016

0 Response to "FATAWAR RABON GADO (47) DR.JAMILU ZAREWA"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel