IDAN MAMACI BA SHI DA YA'YA ,ZAI IYA WASIYYA DA DUKKAN DUKIYARSA

Ku Tura A Social Media

IDAN MAMACI BA SHI DA 'YA'YA, ZAI IYA WASIYYA DA DUKKAN DUKIYARSA ?

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Da Allah malam Ina da tambaya kamar haka: shin saurayin da bai yi aure ba, amma yana da iyaye da 'yan'uwa a raye, zai iya yin wasiyya da rabin dukiyar shi, kasancewar  ba shi da 'ya'ya ?  Nagde

Amsa:

A zahirin hadisai ingantattu har wanda ba shi da 'ya'ya ba zai yi wasici da sama da daya daga cikin uku na dukiyarsa ba, saboda Annabi s.a.w yana cewa da Sahabinsa Sa'ad (RA) lokacin da ya so ya yi wasiyya da mafi yawan dukiyarsa: "Ka bar magadanka cikin wadata, ya fi ka bar su matalauta suna rokon mutane".                                                              
Kasancewar Annabi (S.a.w) ya yi amfani da lafazin magada, hakan sai ya nuna ko ba 'ya'ya ba za'a yi wasiyya da sama da daya cikin uku na dukiya ba, saboda hakan zai cutar da ragowar magada, ya iya jefa su cikin talauci bayan mutuwar magajinsu.                           

Aya ta: 12 a cikin suratu Annisa'i tana nuna cewa: Wanda zai mutu ba shi da 'ya'ya, ba shi da iyaye, ba zai yi wasiyya da abin da zai cuci magadansa ba.

Allah ne mafi sani.

Amsawa: Dr Jamilu zarewa.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"

Adam A. Zango yayi kira ga General BMB da ya dena kula masu zaginshi"Basu da ko sisi"