ALAMOMIN DAUKEWAR JININ HAILA!

Ku Tura A Social Media

ALAMOMIN DAUKEWAR JININ HAILA !

Tambaya:

Assalamu alaikum. Allah ya kara MA Mallam Basira.

Malam tambaya ta akan jinin haila ne. Malam an ce alaman da ake gane karshen haila shi ne idan jinin ya canza kala zuwa ruwan kasa.

Na ga alaman hakan Se nayi wankan tsarki Bayan haka Se kuma ya cigaba da zuba na kwana biyu Malam tsarkin nawa yayi? Yaya matsayin sallah da azumi? Nagode.

Amsa:

To 'yar'uwa abin da na sani daga malaman fiqhu shi ne:

Ana gane daukewar jinin haila ne ta hanyoyi guda biyu:                     

1- Kekasar kasanki-Ta yadda mace za ta ga gabanta ya bushe ko kuma tsumma ko always din da ta tare jinin da shi.                                                              
2- Fitowar farin ruwa bayan daukar lokaci ana haila.                                                                             
Idan jininki ya koma ruwan kasa kafin ki ga daya daga cikin wadannan alamomi guda biyu, to ba ki gama haila ba, kuma ba za ki dauki hukuncin masu tsarki ba, don haka azuminki da sallarki  ba su yi  ba.                                                                                  Idan kika ga ruwa mai kama da kasa bayan daukewar jinin haila, to ba zai cutar da tsarkin da kika samu ba, kamar yadda hadisin Bukhari daga Ummu Addiya ya tabbatar da hakan.
Don neman karin bayani duba: Addma'uddabi'iyya shafi na: 14.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu zarewa.                                                         10/7/2016

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"