DR. NAZIFI JOS YANA CIKIN MAWUYACIN HALI, INJI IYALINSA

Ku Tura A Social Media

Dakta Nazif Jos Yana Cikin Mawuyacin Hali, Inji Iyalinsa
Daga Saleh Aliyu
Iyalan fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan da ke Jos, Dakta Nazeef Muhammad Yunusa da ke tsare a hannun hukumar DSS, sun koka matuka game da mummunan halin rashin lafiya da yake fama da ita.
Mai dakin Shehin Malamin, Hajiya Saudatu Yunusa ce ta yi wannan kukan a lokacin da take zantawa da manema labarai. Ta ce halin da yake cikin abin damuwa ne matuka.
Dakta Nazeef Yunusa, wanda fitacce Malamin Salafiyya ne, an kama shi ne a ranar 29/10/2013 a gidansa da ke Unguwar Rogo a Karamar Hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, bisa zargin da ake masa na shigar da mutane cikin kungiyar Boko Haram. Kamun nasa ya biyo bayan kama wasu dalibansa hudu ne da aka yi a jihar Kogi.
Hajiya Saudat, wacce ke bayani cikin kuka, ta tabbatar da cewa wasu majiyoyi masu tushe daga inda ake tsare da shi, sun tsegunta masu cewa Shehin Malamin yana fama da matsananciyar rashin lafiya.
Ta ce; 'Ko lokacin da aka kama shi ya shaida masu ba shi da lafiya yana bukatar kulawar Likitoci saboda Ulcer da hawan jini da yake fama da su. Ya kamata ya bayyana a gaban kotu ranar Larabar da ta wuce, kuma bai bayyana ba saboda rashin lafiyar da yake fama da ita'.

Comments

Popular posts from this blog

Alamomi Guda 9 Yadda Zaka Gane Idan Budurwanka Bata Sonka Ko Baya Sonki

Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin Maye

Album : Ɗan Adam A Zango Haidar A Zango Ya kamala Shooting Album Dinsa Mai suna " Take Over"

Ina tare dake a cikin daukaka da rashinta' - Inji Adam A. Zango ya gayawa Zainab Indomie

Kalli Hotunan Taurarin kwallon kafa 31 musulmai da zamu yi azumin watan Ramadana tare dasu

Maryam Gidado zata yi aurene?: Kallarta tare da wanda ake sa ran zata aura

Umar M Shariff & Abdul D One - Yar Budurwa Album ft Mohd Mai Lerey

MUSIC : Sabuwar Wakar Rarara " Akan Tsayawar Buhari Takara 2019"