Latest Post
Yunkurin Tozarta Dan takarar Shugabancin kasar nan Atiku Abubakar a Filin jirgin sama ya samu tasgaro ta yadda a ka yi amfani da jami'an tsaro wajen yunkurin Sanya masa Kudaden Kasashen Ketare domin cimma wata manufa ta daban.

Tsohon mai magana da yawun jam'iyyar APC Kwamared Timi Frank, shi ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce an yi kokarin Bata Sunan Dan takarar Shugabancin Kasar nan a lokacin da ya sauka Najeriya daga Kasar Dubai. 

Frank ya cigaba da cewa Atiku, wanda ya dawo yau Lahadi da Misalin karfe 1 na Rana daga Hutun da ya tafi a can kasar ta Dubai saukar sa ke da Wuya sai muka ga jami'ai na Musamman sun sauka suna Binkicen jirgin da Atiku ya fito  tare da daukar faya-fayen Bidyo da Hotuna a cikin jirgin da wajen sa.

Bayan sun gama duk binkicen su na tsawon lokaci basu ga komai a jikin Atiku Ko cikin jirgin sa ba duk da sun yi kokarin ajiye wata jaka makare da kudaden kasashen waje gami da wasu kaya na laifi amma dai Shirin nasu ya samu cikas Inji shi. 

Ya kara da cewa dama dai sun shirya shirin ne Idan Atiku Ya sauka Najeriya sai a nu na ma duniya cewa ya zo da wasu kudade da kuma wasu kayan laifi duk da mun san Yanzu haka Fadar Shugaban Kasa tana Cikin Alhinin rashin yin nasara a wannan shiri na Bata Atiku da ta kwashe lokaci tana kitsawa.

Frank ya ce don haka muna Allah wadai da wannan yunkuri na fadar Shugaban Kasa karkashin Jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari tare da yi masa tuni da cewa da tsohon shugaban kasa Ebele Johnathan ya yi masa irin wannan a zaben 2015 ai da bai zama shugaba ba a yau. 

Kazalika ya ce tun lokacin da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Ya yi Mulki Shekaru Takwas yau ne na farko da a ka fara caje jikin sa a filin sauka da tashin jiragen Sama a duk duniya. 

Ya kuma ce muna gargadi ga fadar shugaban kasa da cewa ta kama Mutuncinta kuma ta guji yin duk wani Shiri na Bata Sunan dan takarar jam'iyyar PDP.

Domin muna da wani labari daga majiya mai tushe na irin kulle-kullen da kuke yi game da Dan takararmu don haka muke kira da Babbar Murya ga Hukumar Sanya Idanu ta kasa da Kasa da su duba wannan Al'amari da idon basira na yadda a ke Tsorata dan tarakar adawa wanda ya yi Mataimakin Shugaban Kasa tsawon Shekaru 8.

Sa Hannu:
Kwamared Timi Frank
Tsohon Mataimakin Sakataren yada labarai na APC.

Jaridar Dimokuradiyya 11/11/2018.

An Gano Wani Chochi Inda Yan Mata Da Matan Aure Ke Tubewa Zindir Domin Yin Ibada

Yansanda sun bankado wani abin mamaki bayan sun gano wani Chochi inda Mata masu ibada suke gudanar da bauta zindir haihuwar Uwarsu.bancin shi Pasto na Chochin wanda shi kadai ne na miji. Wannan lamarin ya faru ne ranar Talata a garin Rukiga da ke Arewacin  kasar Uganda.

Majiyarmu ta ce, wannan Chochi gidan shi Pasto ne mai  suna  Adah Kahababo, kuma yawancin Mata da ke ibada zindir a cikin Chochin, matan aure ne da suka baro Mazajensu suka je wannan Chochi  inda ake ibada zindir.

Sai dai Kwamishinan yansanda na yankin Emmy Ngabirano, ya baiyana matukar mamaki yadda wadannan Mata ke ibada dare da rana kuma zindir a cikin wannan Chochi, da Kwamishinan ya ce baya da rijista da ya bashi izinin gudanar da bauta.Sakamakon haka, Kwamishina Emmy Ngabirano ya ce Mata da aka kama a cikin wannan Chochi, suna gudanar da haramtacciyar taro ne a gidan wanan Pasto.

Hadaddiyar rundunar jami’an tsaro ne suka kai samame a wannan Chochi, bayan an rada masu bayanan sirri, kuma suka cafke dukannin mata da aka samu a cikin wannan gida da ake kira Chochi wajen da Mata ke tubewa zindir domin su yi ibada dare da rana.

Amsar Da Rahama Sadau Ta Bawa Wani Da Yacce Zai Aure Ta

Fitacciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi addu’a ga wani “masoyinta” wanda ya roki Allah ya ba shi matar kamarta.

Shi dai Khamisu S. Guyaba ya wallafa sako ne a shafin Twitter inda ya nuna matukar son da yake yi wa Rahama domin ya aure ta.

Sai dai ya kara da cewa idan hakan ba za ta yuwu ba yana so ya auri mai hali da ilimi da nutsuwa da kuma taimakon jama’a kamarta.
Masu bibiyarsa a shafin Twitter sun taya shi addu’a inda wasu ke cewa Allah ya cika masa burinsa yayin da wasu ke yi masa addu’ar zabi mafi alheri.

Daga bisani ne jarumar ta ba shi amsa inda ta roki Allah ya ba shi matar da ta fi ta sannan ta yi masa godiya.

“Allah ya ba ka wacce ta fi Rahama da komai. Na gode sosai,” in ji jarumar.


Domin Kallon Videon wannan Amsar tambayar A YouTube kai tsaye sai ku danna  hoton dake kasa


Jaruma Fati  Abubakar wanda anka fi sani da fati shu'uma ta samu kyatar latsa gwarzowar shekara ta 2018, na ban dariya a cikin fim din Bintoto,wanda arewa night award ta karamata akan bada gudumuwar na nishadar da mutane da tayi.

Ga jawabin godiya daga jarumar


"AREWA NIGHT AWARD 2018 presented to FATI SHU'UMA best comedian BINTOTO in recognition of your contribution to the Entertaiment industry thank u so much ❤❤"

An cewa Amina Amal tana kama da Aljana kuma bata iya kwalliya ba: Ta kukkun duma zagi

Jarumar fina-finan Hausa, Amina Amal ta gamu da wasu da suka gayamata maganar da ba taji dadinta ba inda har suka kure hakurinta ta kukkun duma musu zagi, Amina ta saka wannan hoton na kasa, sai wata tace mata bata iya kwalliya ba, taci gaba da gayamata kananan maganganu marasa dadi.

Amina kuwa ta kasa jurewa ta mayar da magana cikin fushi hadda kundumemen zagi.

Bayannan kuma Aminar ta sake saka wancan hoton na farko, yayin da kowa ke yabawa, wani shi kuma sai yace ai tayi kama da Aljana, wannan ma ya kara hasalata shima ta bashi rabonshi na zagin.
Mutane dai sunyi bata baki ana cewa ta daina kula masu sukarta tunda duk inda akace ka zama wani to dolene sai kayi hakuri da jama'a. Amma Amina ta kare zage-zagen da tayi inda tace itama fa mutumce idan an mata ba daidaiba dole taji zafi.
Ga yanda maganganun suka kasance:An sace wasu ‘yan mata tagwaye lokacin da suke kan hanyarsu ta kai wa ‘yan uwa da abokan arziki ankon bikinsu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Mataimakin Shugaban karamar hukumar Zurmi Abubakar Muhammad ya ce tagwayen wadanda ake shirye-shiryen aurensu suna cikin mutane bakwai da aka sace a garin Dauran da ke jihar ZamfaraZamfara.

“A tsakanin ranakun Asabar zuwa Lahadi ne aka sace mutanen bakwai – wato maza hudu, mata uku.

“Nan kusa gare mu ma an sace namiji guda, mace guda wato nan Birnin Tsaba ke nan,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: “A garin Moriki an ma an dauki mutum uku da wadansu da aka sace ciki har da wani kansila.”

Har ila yau ya ce an yi magana da masu garkuwa da mutanen kuma sun bukaci a “biya su naira miliyan 100 kafin su sako ‘yan tagwayen.”

Daga nan ya bukaci da a kawo musu dauki don kawo karshen matsalar.

Zamfara tana daya daga cikin jihohin arewacin kasar da ke fama da matsalar tsaro.

BBC HAUSA

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.